30 Yuni 2014 - 14:36
Kungiyar Da'ish Ta Kafa Daular Musulunci Ta Duniya Karkashin Jagorancin Shugabanta

Kungiyar Da'ish Ta Kafa Daular Musulunci Ta Duniya Karkashin Jagorancin Shugabanta

Kungiyar daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish ta shelanta kafa daular Musulunci tare da sanar da shugabanta Abubakar Baghadadi a matsayin shugaban musulmin duniya.

A jawabin da Abu-Muhammad Adnani kakakin kungiyar Da’ish ya fitar a jiya Lahadi yana dauke da cewa; Manyan mashawartan kungiyar Da’ish sun sanar da kafa daular Musulunci ko kuma Khilafa Islamiyya tare da gudanar da mubaya’a ga Ibrahim Awwad Ibrahim Al-Badri Al-Samarra’i da aka fi sani da Abubakar Baghadadi dan shekaru 43 a duniya a matsayin khalifan musulmin duniya.

Jawabin ya kara da cewa; daga yanzu an maye gurbin daular Musulunci a Iraki da Sham da sunan daular Musulunci ta duniya karkashin khalifancin  Abubakar Baghadadi, kuma wajibi ne a kan dukkanin musulmin duniya su yi masa mubaya’a tare da taimaka masa.

Wannan mataki na kungiyar Da’ish ya bayyana a fili karara cewa; kungiyar ta yi tawaye ga babban kungiyar ta’addanci ta Al-Qa’ida karkashin jagorancin Aiman Al-Zawahiri da ya karbi ragamar shugabancin kungiyar Al-Qa’ida a bayan mutuwar Usama bin Ladan.ABNA